Wasu yan bindinga da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne, sun sace wani magidanci dan shekaru 46, mai suna Alhaji Musa Garba Atere, kuma sun bukaci kudin fansa miliyan N30 daga dangin su don sakin shi a Jihar Kwara.
An bayyana cewa an sace Atere da misalin karfe 6:00 na safe a ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu, akan hanyar Ogundele / Madi a karamar hukumar Ilorin West.
An ce yana kan hanyarsa ta zuwa Babban Asibiti, Ilorin tare da matarsa da ’yarsa’ yar shekara takwas wanda bata da lafiya kuma tana bukatar agajin gaggawa lokacin da ’yan bindigar suka yi musu kwanton bauna.
Wata majiya daga dangi, wacce ta tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin, ta ce daga baya masu garkuwar sun kira matar tasa, sun nemi N30m a matsayin kudin fansa.
Yayin da take bayar da labarin abin da ya faru, matar wanda lamarin ya rutsa da shi, ta ce masu garkuwar su shida ne, sun tare musu hanya tare da neman kudi.
Tace sun tarbata abunda ke hannun su sun basu, amma duk da hakan suka yi awon gaba da mijinta.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya ce tuni’ yan sanda suka fara gudanar da bincike a kan lamarin.