fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Yan Bindiga Sun Sace Wasu Fasinjoji 18 a jihar Niger

Wasu ‘yan fashi sun sace fasinjoji 18 dake tafiya a motar Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Neja (NSTA).
Harin ya auku ne a kauyen Yakila da ke karamar hukumar Rafi a jihar a ranar Lahadi.
An ce fasinjojin suna zuwa Minna, babban birnin jihar daga Kotangora lokacin da lamarin ya faru.
Babban Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Malam Ibrahim Inga, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Inga, wanda ke kan hanyarsa daga Kagara don sabunta rigistarsa na jam’iyyar APC, ya ce sun ziyarci wurin da ‘yan fashin suke aiki.
Ya bayyana cewa sun hadu da wata mata tare da yaronta wanda barayin suka bar shi amma an tafi da wasu fasinjoji 18.
“Abin da kawai zan iya fada muku yanzu shi ne mun ceto matar da jaririnta kuma tana cikin motar tare da mu kuma muna kan hanyar zuwa Minna.
“Ta fada mana cewa‘ yan fashin sun tare hanya sun tafi tare da wasu fasinjoji 18 a cikin motar bas din.
“Babu wani jami’in gwamnati a cikin wadanda aka sace. Ba zan iya bayar da sama da haka ba a yanzu saboda matar ta shiga damuwa kuma ba za mu iya yi mata tambayoyi da yawa a yanzu ba, ”in ji Inga.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, Wasiu Abiodun, bai dauki wayarsa ba ko amsa sakonnin.

Bandit just attack NSTA bus this afternoon for Yakila along zungeru road, carry 21pipu wey dey inside the boss go except one woman with her pikin according to eyes witness.

 

This happened around 3pm today around Kundu in yakila district RAFI LGA NIGER STATE. They were passengers from Rijau LGA to Minna All in Niger State.

 

List of persons Kidnapped in the NSTA Bus.

Talatu, jummai,larai Halima Aisha ya Fati,Sala,Saadatu,HauwaAsmamau,Hassana,Maryam,Nafisa,Abdulkadir,Hassan,Sadiq,Babakarami, Mama Iye
Mama jummai
Mama larai
Hauwa abdlsm
Asmau abdlsm
Mama Halima
Anty ladidi
Hassan Ashiru
Baba kararami
Sadiq abdlsm
Hassana abdlsm
Abba abdlsm
Nafisa Adamu
Saadatu Danjuma
Salamatu Danjuma

NSTA NO 8, Driver’s name Alh Isa Dangana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *