‘Yan Bindiga sun sako fasinjojin jirgin kasan da suka kama a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Sun sako maza 5 da mata 6 cikin wadanda suka kama din.
A ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata ne dai aka kama mutanen bayan kashe wasu. An sako fasinjojin ne a yau, Ranar Asabar.
Mawallafin jaridar Desert Herald, Tukur Mamu wanda shine ya shiga tsakani ya tabbatar da sakin wadanda aka sace din.