fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

‘Yan bindiga sun sako malaman majami’a guda biyu da sauran mutanen da sukayi garkuwa dasu a cocin Bishop Kukah

‘Yan bindiga sun saki malaman majami’a guda biyu da sauran mutanen da sukayi garkuwa dasu a cocin katolika ta Bishop Kukah dake karamar hukumar Kafur a jihar Katsina.

A ranar 25 ga watan mayu na shekarar 2022 ne ‘yan bindigar suka afka cocin sukayi garkuwa da malaman guda biyu tare da wasu mutane.

Amma yanzu an sako su kamar yadda mai magana da yawun cocin katolika ta jihar Sokoto, Rev. Fr Christopher Omotosho ya bayyana yau lahadi.

Kuma yace suna godiya ga mutanen da suka taya su da addu’a malaman nasu da sauran mabiyansu suka dawo ga iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.