fbpx
Friday, July 1
Shadow

‘Yan bindiga sun sako mutane 29 da sukayi garkuwa dasu a jihar Zamfara

A ranar 13 ga watan yuni ‘yan bindiga sukayi garkuwa da wasu mutane 29 kan hanyar Zamfara zuwa Gusau yayin da suke dawowa daga shagalin biki.

Kuma rahotanni sun bayyana cewa mutanen ma’aikatan kamfanin layukan waya ne na GSM.

Kuma yanzu sakataren kamfanin layukan wayar na Gusau, Ashiru Zurmi ya bayyana cewa an sako su a ranar 23 ga watan yuni, amma bai ce an biya kudin fansa ba.

Duk da cewa dai a kwanakin baya ‘yan bindigar sun bukaci a bayar da naira miliyan 140 kafin su sako su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.