fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

‘Yan bindiga sun sako mutane uku cikin mutanen da suka lallasa a sabon bideyon da suka saki na fasinjojin jirgin kasa

‘Yan bindigar da sukayi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa na jihar Kaduna sun sako mutane uku, a cikinsu maza biyu da mace guda.

Channels TV ne suka ruwaito wannan labarain inda suka kara da cewa ‘yan bindigar sun kaisu kan babbar hanyar jihar Kaduna inda ‘yan uwansu suka je suka dakko su.

A ranar lahadi ‘yan bindigar suka saki sabon bideyo suna lallasa mutanen da sukayi garkuwar dasu kuma har sukayi barazanar kashe su idan har gwamnatin tarayya bata biya masu bukatunsu ba.

Karanta wannan  Rundunar sojoji hadin kai sun hallaka 'yan bindiga takwas a jihar Filato

Har yanzu dai akwai sauran mutane kusan 40 a hannun ‘yan bindigar kuma izuwa yanzu sun sako mutane 22.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.