Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da ‘yan uwa shugaban jam’iyyar PDP ta Kajuru a jihar Kaduna sun sake su.
An sako ne a daren ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu, makonni bayan sace su.
Wadanda aka sace sun hada da Joseph Barde, Gambo Barde, Obadiah yohanna Barde, Bamaiyi Joseph Barde, Blessing yohanna Barde, Jennifer yohanna Barde, Salama Gombo.
Tun farko dai an sako daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su bisa dalilai na rashin lafiya, yayin da ‘yan fashin suka nemi kudin fansa domin a sako sauran.
Daga baya ‘yan bindigar sun kashe daya daga cikinsu saboda gazawar da iyalan suka yi wajen biyan bukatunsu.
Yanzu haka dai sun saki sauran mutane biyar din da suka hada da; Obadiah Barde, Bamaiyi Joseph, Salama Gambo, da Jennifer Yohanna.