‘Ya bindiga sun tare babbar hanyar Enugu zuwa Patakwal inda suka babbaka motar sojoji kuma suka yi garkuwa da wasu fasinjoji.
Wannan lamarin ya faru ne a karshen makon daya gabata, inda ‘yan bindigar suka tare wasu motocin haya guda uku akan babbar hanyar.
Kuma an sanar da rundunar soji domin su kawo dauki amma ‘yan bindigar suka bude masu wuta suka jiwa sojoji biyu rauni cikinsu.
Kafin daga bisani suka tsere da fasinjojin cikin daji.