fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Yan bindiga sun yi barazanar auren wata mace mai shekaru 21 idan iyayenta suka kasa biyan kudin fansa N1.7m

Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da wata mata ‘yar shekara 21 tare da wasu a hanyar Tapila-Gwada, wani yanki da ke karamar hukumar Shiroro ta Nijar, sun yi barazanar aurenta.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne kan al’ummar da ke kusa da Minna, babban birnin Nijar da yammacin ranar Asabar 16 ga Afrilu.

‘Yan bindigar wadanda da farko sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan biyu, sun mayar da bukatarsu zuwa N1.7m bayan sun yi magana da iyayen yarinyar a daren ranar Talata.

Rahotanni sun ce sun bukaci iyayen yarinyar da aka sace mai suna Deborah da su biya Naira miliyan 1 a matsayin kudin fansa, sannan su saya musu babur kan Naira 750,000.

Karanta wannan  Kotun jihar Ondu ta yankewa wani mutun hukucin watanni 12 a gidan yari saboda lalata da wata yarinya yar shekara 15

Theresa, yayar matar ta ce; “Wadannan mutane suna neman kudin fansa nera miliyan daya, sannan sun bukaci 750,000 domin su sayi babur ko kuma su aurar da ita ga daya daga cikinsu.

Wasiu Abiodun, kakakin rundunar ‘yan sanda a Nijar wanda ya yi tsokaci kan harin, ya ce sun samu nasarar dakile harin tare da dawo da zaman lafiya a cikin al’umma kuma har yanzu ba su gama hada bayanai kan lamarin ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.