fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mata mai cikin wata tara a jihar Zamfara

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da matar tsohon shugaban NULGE a jihar Zamfara, Alhaji Sanusi Gusau.

Sunyi garkuwa da matar ne, Rahmatu Yunusa da safiyar ranar talata a gidansa dake Damba a jihar, kuma ysna dauke da cikin watanni tara.

Inda mai gidan nata, Alhaji Sanusi Gisau yace baiji yadda wannan lamarin ya faru ba domin babu wanda ya kawo masu dauki hatta jami’an tsaron dake yankin.

Yace sun afka gidan nasa ne da misalin karfe daya na dare kuma ya san shi suka je kamawa, amma Allah yasa yayi nasarar boyewa basu ganshi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.