fbpx
Sunday, August 7
Shadow

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da matan aure hudu tare da ‘yan uwnsu biuyar a jihar Katsina

‘Yan bindiga sun kai hari kwatas din Shema dake karamar hukumar Dutsinma a jihar katsina ranar lahada da daddare.

Inda suka yi garkuwa da matan aure guda hudu tare da wasu mutane biyar, yayin da su kuma mazajensu suka tsere saboda kar su kashe su.

‘Yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 11 na dare yayin da ake ruwan sama mai karfi kuma sun dauki tsawon awanni uku suna ta’addancin nasu.

Kafin daga bisani bayan sun wuce hukumar ‘yan sanda tazo wajen, kuma mai magana da yawun hukumar Isa Gambo ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.