‘Yan bindiga sunyi garkuwa da matar shugaban karamar hukumar Magama, Usman Baffa Ibeto dake jihar Niger.
Usman Baffa Ibeto ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar mulki ta APC a jihar.
‘Yan bindigar sunyi garkuwa da ita ne a gidanta dake Tunga a babban birnin Niger wato Minna,
Kuma har yanzu basu kira ‘yan uwanta sun bukaci kudin fansa ba.