fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane biyu suna tsaka da bauta a cocin jihar Ogun

‘Yan bindiga sun kai hari cocin calestial dake karamar hukumar Ewekoro a jihar Ogun suna tsaka da bauta.

Yayin sukayi garkuwa da ‘yan cocin guda biyu da sukaje bauta da safiyar ranar talata kuma hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar, Abimbola Oyeyemi ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari cocin ne suna tsaka da bauta,

Inda sunyi garkuwa da mutane biyu kuma hukuma na iya bakin kokarinta don ganin cewa ta ceto mutanen da akayi garkuwar dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.