fbpx
Monday, August 15
Shadow

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane hudu a jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun mamaye kauyen Shika dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, inda sukayi garkuwa da mutane hudu.

‘Yan bindigar sunyi garkuwa da matar malamin kwalejin Polytechnic ne ta Nuhu Bamalli wato Malam Umar tare da yaransa guda uku.

Kuma ‘yan vigilanti sunyi nasarar korarasu bayan sunyi garkuwa da mutanen, inda sukayi musayar wuta kafin su tsere.

Shugaban Karamar Giwa, Alhassan Zico ya tabbatar da kai wannan harin da kuma garkuwar da mutanen inda ya jinjinawa ‘yan vigilanti bisa kokarin da suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.