‘Yan bindiga a daren ranar talata sun kai hari makarantar Statistics dake jihar Kaduna a karamar hukumar Kaura inda suka kashe mutun guda,
Kuma sukayi garkuwa da wasu mutane biyu duk dai a makarantar ta Manchok, wanda a cikinsu hadda Rector na makarantar wato shugaban makarantar kenan.
Wannan lamarin ya faru ne bayan makonni uku da suka gabata ‘yan bindigar sun kashe wasu ma’aikatan gwamnatin dake raba sange wato Mosquito nets a karamar hukunar.