Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar Bauchi, Ahmed Wakil ya bayyana cewa ‘yan bindiga sunyi garkuwa da mai garin kauyen Zira a karamar hukumar Toro.
Yahya Abubakar, wanda ya kasance mai garin anyi garkuwar da shine tare da yaronsa da misalin karfe 2 na dare a ranar asabar.
Kuma hukumar tace ta fara gudanar da bincike domin gano inda suke kuma a ceto su.