Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta tabbatar da sace wani saurayi a yankin Effurun, dake karamar hukumar Uvwie a jihar Dalta.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Onome Onovwakpoyeya shine ya ba da tabbacin ga manema labarai a ranar Juma’a, a Warri Inda ya shaida cewa Lamarin ya faru ne a tashar Ugborikoko da yammacin ranar Alhamis.
A cewarsa rundunar tana cigaba da bincike domin kubutar da Wanda aka sace.