‘Yan Bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasar dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja sun bayyana cewa zasu fara kashe wanda suke tsare dasu.
Sun ce zasu dauki wannan mataki ne saboda gwamnati ta kasa cika musu bukatun da suka nema.
Dan hakane sukace sun baiwa gwamnatin kwanaki 7 nan gaba a biya musu bukatunsu ko su kashe wadanda suke rike dasu.
Bukatarsu shine a saki iyalansu da kwamandojinsu dake hannun Gwamnati.