fbpx
Saturday, May 28
Shadow

‘Yan Bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasan Kaduna sun saki matar dake da ciki

Ƴan bindigar da suka kai harin bom a jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna sun saki matar da ke da ciki daga cikin fasinjojin da suke garkuwa da su.

An sako matar ne saboda dalilai na jin-kai, kamar yadda Kwamishinan tsaro da harakokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar wa BBC.

Sai dai ya ce har yanzu ba su ido biyu da matar ba, amma ya ce gwamnatin Kaduna a shirye ta ke ta kula da ɓangaren kiwon lafiyarta.

Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta wanda jaridar Daily Nigeria ta wallafa, ya nuna wata mata sanye da hijabi da takunkumin fuska tana bayanin cewa ita ce mai ciki daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa.

A cikin bayaninta ta ce: “Sun ji tausayi na sun sake ni saboda halin da nake ciki.”

Ta ce maharan da suka yi garkuwa da su sun ba su kulawa tare da ciyar da su abinci har a cikin azumin watan Ramadan.

Kusan wata biyu kenan da wasu ƴan bindiga da ake tunanin mayaƙan Ansaru ne suka kai wa jirgin ƙasa hari da ke jigilar fasinja daga Abuja zuwa Kaduna ta hanyar ɗąna bom a kan hanyar jirgin a watan Maris.

Mutum aƙalla takwas aka kashe a harin, yayin da har yanzu ba a san makomar mutum 167.

A watan Afrilu ƴan bindigar sun fitar da bidiyo ɗauke da bindigogi suna iƙirarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin ƙasan inda kuma suka saki shugaban Bankin noma Alwan Hassan ɗaya daga cikin waɗanda suka sace.

A cikin masu jawabi a bidiyon ya ce ba buƙatar kuɗi ce ta sanya su sace fasinjojin ba, yana mai iƙirarin cewa gwamnati ta san buƙatunsu.

Ƴan bindigar sun ce ba za su saki mutanen ba har sai gwamnati ta biya musu buƙatunsu, amma ba su bayyana buƙatun nasu ba.

Maharan sun ce sun saki Alwan Hassan ne saboda tausayin tsufa da kuma alfarmar azumin watan Ramadan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.