‘Yan bindigar da sukayi garkuwa da mutane hamsin a hanyar Sokoto zuwa Gusau sun bukaci a basu kudin fa sa har naira miliyan 145 kafin su sako su.
Mutanen da ‘yan bindigar suka kama ma’aikatan kamfanin layin waya ne na GSM, kuma sunyi yi garkuwa dasu ne a Dogon Awo yayin da suke dawowa daga wani shagalin biki da suka halatta.
‘Yan bindigar sun ce zasu karbi naira miliyan biyar akan kowanne daga cikinsu kuma ba zasu sakosu daban daban ba, duk a tare suke so su sako su.
Amma wasu jajirtattun ‘yan banga sun fara ceto su inda sukayi ta maza suka kwato har mutane bakwai a cikin su.