fbpx
Monday, June 27
Shadow

’Yan Bindigar Da Suka Sace Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Nasarawa Sun Sako Shi

’Yan bindigar nan da suka yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Keffi da ta Jihar Nasarawa, Baba Shehu tare da direbansa, Tanimu, sun shaki iskar ‘yanci.

Aminiya-trust ta rawaito cewa, majiyarsu wacce ke da kusanci da wadanda lamarin ya shafa ta ce an sako su ne ranar Asabar da misalin karfe 12:00 na dare bayan biyan kudin fansa na Naira miliyan N10 da dubu 200.

Tuni dai suka iso gidajensu cikin koshin lafiya.

Yayin harin dai, maharan sun sace Shugaban Karamar Hukumar ne tare da harbe dogarinsa, Alhassan Habeeb, har lahira.

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da dare a hanyar Akwanga zuwa Gudi, a lokacin da suke kan hanyarsu ta komowa Keffi daga Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa:Gwamnatin jihar Zamfara tace kowa ya kowa ya sayi bindiga ya rika kare kansa don ta gaji da matsalar tsaro

Rahotanni daga jihar sun ce maharan sun kira suna neman a biya su Naira miliyan 30 kafin su sako Shugaban Karamar Hukumar Keffin tare da direbansa, Tanimu Senior Man da suke hannunsu.

A ’yan kwanakin nan dai rahotanni sun nuna masu garkuwa da mutane sun matsa wa hanyar Gudi zuwa Akwanga inda suka yawaita kai hare-hare a yankin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.