‘Yan bindigar da sukayi garkuwa da mutane uku ‘yan garin Akaram dake karamar hukumar Akoko a jihar Ondo sun bukaci kudin fansa naira miliyan 40 a hannun iyalansu.
‘Yan bindigar sunyi garkuwa dasu ne a garin Ayere yayin da suke yin tafiya daga jihar Kogi zuwa Ondo, inda suka tafi dasu cikin jeji.
Kuma yanzu sun kira ‘yan uwansu cewa su biya kudin fansa naira miliyan 40 kafin su sako su daga sansaninsu.
Yayin da ‘yan uwansu suka bayyana cewa suna cigaba da sasantawa da ‘yan bindigar don su rage kudin fansar.