Gwamnatin Chadi ta fitar da alkaluman da ke cewa dakarunta 52 ne suka rasa rayukansu yayin da mayakan Boko Haram sama da dubu daya suka hallaka a fadan da aka share tsawon kwanaki ana gwabzawa tsakanin bangarorin biyu a zagayen tafkin Chadi.
Kakakin Rundunar Sojin kasar, kanar Azem Bermendoa Agouna, ya ce baya ga kashe mayakan na Boko Haram sama da dubu daya, an kuma lalata babura da kuma kananan jiragen ruwan da ‘yan ta’addar ke amfani da su don kai farmaki.
Wannan ne dai karon farko da rundunar sojin kasar ta Chadi ta sanar da yawan dakarunta da suka mutu bayan kaddamar da farmaki kan mayakan na Boko Haram da ta yi wa take da ‘fushin Bohoma.’