Rundunar sojin Najeriya ta dakile harin da mayakan Boko Haram Suka yi yunkurin kaiwa a garin Gaidam na jihar Yobe a jiya,Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa,Boko Haram din basu ji dadadi ba a hannun sojojin na rundunar Operation Lafiya Dole inda suka hanasu cimma burinsu na kaddamar da hari a Geidam.
Rahotan yace an kashe ‘yan Boko Haram din su 13, sannan an kwato bindigogi AK47 guda 6 da motocin yaki 2.
Babu dai soja ko daya da aka kashe a harin.
Hakanan hukumar sojin ta bayyana cewa, nan gaba kadan shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau zai mika wuya saboda bashi da gurin Buya.
Hakanan me magana da yawun hukumar tsaron,Majo Janar John Enenche ya bayyana cewa akwai mayakan Boko haram din da dama dake mika wuya.
VIDEO: Coordinator, Defence Media Operations @DefenceInfoNG, Maj Gen John Enenche says:
Boko Haram fighters surrendering en-masse, & Nigerian military duty-bound to obey international law regarding SURRENDERING belligerents: Take them as prisoner of war & treat them humanely (1) pic.twitter.com/kqe5OdLivf
— tolu ogunlesi (@toluogunlesi) April 20, 2020
Ya kara da cewa idan suka yi saranda za’a karbesu haka dokar yaki ta kasa da kasa ta tanada.
Personally, I comment the effort of our gallant soldiers, this is what we have been expecting long ago.. Go ahead Allah will saw you through.