fbpx
Friday, June 9
Shadow

Yan daba sun fasa rumbun ajiyar kayan tallafin COVID-19 a Ondo, inda suka yi awon gaba da kayan, sannan suka cinna ma Rumbun wuta

Yan daba sun fasa cikin rumbunan ajiyar gwamnati a Akure, babban birnin jihar Ondo, kuma sun wawushe kayayyakin tallafi na COVID-19 da aka ajiye a can.

A cewar rahotanni daga baya suka kone gidan ajiyar.
Gidan ajiyar yana cikin harabar babban kotun majistare a cikin garin Akure.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Gwamnatin Tarayya ce ta baiwa jihar tallafin.
Gwamna Rotimi Akeredolu yayi bikin kaddamar da kayan tallafi na CA-COVID 19 a Akure, babban birnin jihar a ranar 10 ga watan Agustan wannan shekarar.
Bayan samun bayanan sirri, an gano cewa ‘yan daban sun afka cikin dakin ajiyar kayan ne suka fasa kofofin, suka yi awon gaba da kayan.
Sai da sojoji suka shiga tsakani don kawo karshen lamarin a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Wani faifan bidiyo da ya nuna yadda lamarin ya faru a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutane ke tattara jakunkuna da kuma katun din kayan wanda ake sa ran gwamnati za ta raba don magance radadin cutar ta COVID-19.
Kayan sun hada da buhunan shinkafa, sukari, taliyar Indomie da sauran kayan abinci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Hotuna daga ganawar da shugaba Tinubu yayo da gwamnoni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *