Daga Nuruddeen Isyaku Daza ( Minna)
Wasu ‘yan daba sun caka masa wuka a daidai lokacin da yake kokarin siyan katin waya a gaban wani shago a Unguwar Limawa dake Minna Babban Birnin Jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a daren Alhamis din nan, inda majiyar mu ta gano cewa kwanaki uku kenen a jere Yan Daba ke cin Karen su babu babbaka a tsakanin Limawa da Unguwar Daji dake Minna.
A kwanakin baya Gwamnatin Jihar Neja ta kama yawancin yaran dake addabar Al’umma, Amma daga baya daf da Sallla ta sako su kuma tun daga nan ne Al’ummar ke cigaba da fuskantar tashe-tsahen hankula.
Tuni Jama’a na Minna suka fara nuna Rashin jindadi akan yadda Gwamnatin Lolo ke sakaci da batun Yan Sara suka.
Daga Rariya.