fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Yan daba sun kashe dan tsohon darakta janar na NTA a Kaduna

Wasu ‘yan daba a daren Laraba sun daba  dan tsohon Darakta Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Alhaji Mohammed Ibrahim, mai shekara 38, an kai harin a kusa da Kawo da ke cikin Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa.

Aminiya ta ruwaito cewa marigayin, Aminu Mohammed Ibrahim, ya dawo daga Kano kuma yana shirin sauka daga motar haya a lokacin da wasu ‘yan daba da ke labe a yankin suka daba masa wuka suka yi awon gaba da wayarsa.
Babban wansa, Kamal Ibrahim, wanda ya tabbatar wa da Daily Trust faruwar lamarin ya ce Aminu kwanan nan ne kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ya dauke shi aiki.
“Ya zo wani lokaci tsakanin 8:30 zuwa 9:00 na dare kuma yayin da yake kokarin samun tasi, wasu yan daba suka daba masa wuka a kirji, kusa da zuciyarsa suka tafi da wayarsa. An kai shi asibiti kuma ya ba wa ma’aikatan asibitin lambar mahaifinmu da tawa don su kira su sanar da mu amma ya mutu yayin da suke kula da shi, ”in ji Kamal.
Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, lokacin da aka tuntube shi ya nemi a ba shi lokaci domin ya tuntubi Jami’in’ Yan sanda na Shiyya (DPO) mai kula da Kawo amma a lokacin hada wannan rahoton, bayanin ba a shirye yake ba.

 

The 38-year-old son of former Director General of the Nigeria Television Authority (NTA), Alhaji Mohammed Ibrahim, has been stabbed to death in by suspected phone thieves in Kaduna.

 

The incident happened on Wednesday, October 28, around Kawo in Kaduna North Local Government Area of the state.

 

It was gathered that the deceased, Aminu Mohammed Ibrahim, was flagging down a commercial vehicle when hoodlums lurking around the area stabbed him and made away with his phone.

 

His elder brother, Kamal Ibrahim, who confirmed the incident on Thursday, October 29, said Aminu was recently employed by Kano Electricity Distribution Company (KEDCO)

 

Aminu received his appointment letter on October 20 and had travelled to Kano for his documentation. He returned to Kaduna on Wedneday night and was trying to get a vehicle home when the hoodlums stabbed him and fled with his phone.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *