Yan sanda a ranar talata sun gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami, wadanda a ranar 22 ga Fabrairu, 2020, suka shiga gidan Ikoyi, wani alkalin Legas, da suka kwace dala 1,000, nera 250,000, agogon hannu hudu, talabijin mai nauyin inci 50, da riguna biyu da takalma biyu.
Wadanda ake tuhumar, Friday Eze da Anuoluwa Adeware – tare da wadanda suka taimaka masu, Rasaq Bolaji da Beatrice Elom, an gurfanar dasu gaban kuliya akan tuhuma guda 15 a babbar kotun tarayya da ke Legas.
Dangane da tuhumar da yan sanda suke yi masa, Eze da Adewale, tare da wani Monday Uvi da sauran wanda da ba’a san inda suke ba har yanzu, sun mamaye gidan alkalin dauke da bindiga, adda da wasu makaman, inda suka kwace masa kadarorin shi.
Masu gabatar da kara sun ce wadanda ake kara sun sabawa Shari’a kuma ana iya yin hukunci a karkashin Sashe na 1 (2) (a) da (b) na Dokar Yan fashi da makami (Bayarwa ta Musamman) na Cap R11 na tarayyar Nijeriya shekara 2004.