‘Yan gudun hijirar Najeriya da ke tsugunne a jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar na fatan sabbin gwamnonin da aka zaba su mayar da su garuruwansu na asali.
A yankin Niger Delta na Najeriya kuwa, an samu matsalolin satar akwatunan zabe, kana ba a gudanar da zaben a wasu sassan yankin ba. Sai dai kuma tuni aka fara fitar da sakamakon zaben yankin. Za mu kawo muku karin bayani kan wadannan batutuwan a shirinmu na rana, ku bayyana mana ra’ayoyinku.
#zabennajeriya2023