fbpx
Thursday, July 7
Shadow

‘Yan Kasuwar Kantin Kwari Dake Kano Suna Cigaba da Tattara Makudan Kudaden da Za Su Turawa Mawaki Rarara

Kungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari dake Kano sun dauki aniyar tarawa fitataccen mawaki Dauda Kahutu Rarara makudan kudade domin ya yi wa Shugaban kasa Muhammad Buhari waka.

 

‘Yan Kasuwar sun kudiri aniyar tattara kudaden guri guda a dunkule, inda kowa zai bayar da tasa gudunmawar ta naira dubu daya. Wanda daga karshe za a tura su a cikin asusun ajiyar banki na Mawakin.

Idan ba a manta ba, Rarara ya bukaci masoya Buhari da su tura masa naira dubu dai-dai kafin ya yi wakar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.