fbpx
Monday, August 15
Shadow

‘Yan kasuwar man fetur sun bijirewa gwamnatin tarayya sun kara farashin litar man fetur zuwa naira 185

‘Yan kasuwar man fetur sun bijerewa farashin da gwamnatin tarayya tace masu su riga sayar da litar mailn fetur inda suke sayar da shi akan ra’ayoyinsu.

Gwamnatin tarayya ta umurci ‘yan kasuwar man fetur na Najeriya cewa su riga sayar da litar man a farashin naira 165.

Amma yanzu ranar alhamis kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ta MOMAN ta koka kan farashin da gwamnatin ta saka masu inda tace ba zasu fita ba idan suka sayar da shi a hakan.

Kuma shima Chinedu shugaban babban kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ta IPMAN,yace farashin gwamnatin ba zai fidda ‘yan kasuwa ba gaskiya, wanda hakan ne yasa yawancin ‘yan kasuwar ke sayar da lita a farashin 185 har ma zuwa 195.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.