Wakilan majalisar dokokin jihar Jigawa sun gabatar da kudirin dokar hana cin zarafin mutane.
Kakakin majalisar, Hon. Idris Garba Jahun ya ce zartar da kudirin zuwa dokan ya biyo bayan karbar rahoton kwamitin majalisar na dindindin kan harkokin shari’a karkashin jagorancin dan majalisar da ke wakiltar mazabar Hadejia, Hon. Abubakar Jallo.
Kudirin wanda ke da shawarwari hamsin da bakwai daga kwamitin kafin a sanya hannu a kansa ya zama doka, ya yi daidai da tsarin addinin Islama da na al’umma da kuma tsarin adalci da aiki.
Sabuwar dokar ta bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin fyade zai daure daurin rai da rai tare da wadanda suka taimaka wajen aikata laifin, yayi da wanda aka yi wa fyade za a ba sa diyyar da ba ta gaza N500,000 ba.
Duk wanda ya yi yunkurin yin fyade za a hukunta shi a kurkuku na tsawon shekara 14 ba tare da zabin biyan tara ba.
Haka ma idan wanda aka yiwa fyaden ya kamu da cutar kanjamau (HIV), to mai laifin zai fuskanci hukuncin kisa.
Har ila yau, a karkashin doka, an hana amfani da munanan kalamai da hotunan tsiraici ga masu sayar da magungunan gargajiyar, kana duk wanda ya sabawa dokar zai fuskanci hukuncin hukuma.