fbpx
Friday, August 12
Shadow

‘Yan majalissar wakilai sun fara amincewa da tsige shugaba Buhari kan matsalar tsaro

Dan majalissar dake wakilatar kudancin jihar Jos, Dachung Bagos yayi Allah wadai kan matsalar tsaron da lasar Najeriya ke fama dashi.

Ya bayyana hakan ne bayan a ranar lahadi ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Danda dake kudancin jihar sun kashe mutane bakwai kuma sun jigata wasu guda biyu.

Inda dan majalissar ya bayyana cewa ya rattaba hannu akan takardar tsige shugaba Buhari don a sauya shi da shugaban na gari da zai iya magance matsalar tsaron Najeriya.

‘Yan bindigar sun kai wannan harin ne kwana guda bayan da suka kai hari karamar hukumar Wase, inda mutabe 18 suka rasa rayukansu yayin da suke musayar wuta da ‘yan vigilanti.

Leave a Reply

Your email address will not be published.