Rahoto ya nuna cewa, kaso 40 cikin 100 na ‘yan Najariya na amfani da janareta wajan aamin wutar lantarki.
Hakanan kuma suna kashe Biliyan 14 wajan sayen man fetur din da suke zubawa a cikin janaretan.
Suna kashe wadannan kudade ne duk shekara saboda rashin wutar lantarki da gwamnati ta kasa samarwa.
An fitar da rahoton ne a watan Yuni na shekarar 2022 inda kuma ya nuna yanda hakn kewa tattalin arzikin Najariya illa.