fbpx
Sunday, August 7
Shadow

‘Yan Najeriya dake kasar Afrika ta Kudu sun jinjinawa gwamnatin tarayya saboda ta magance matsalolin da suke fuskanta a kasar

‘Yan Najeriya dake zaune a kasar Afrika ta Kudu sun jinjinawa gwamnatin shugaba Buhari saboda kokarin datayi na magance masu matsalolin da suke fuskanta a kasar.

Shugaban kungiyar ‘yan Najeriya dake zaune a kasar ta Afrika ta Kudu Mr. Collins Mgbo ne ya bayyanawa manema labarai na NAN hakan a yau ranar laraba.

Inda yace suna mika sakon godiyarsu musamman ga sabon wakilinsu na kasar janar Andrew Idi domin cikin kankanin lokaci ya magance masu matsalolin da suke fuskanta a kasar.

Yayin da kuma suka mika sakon godiyarsu ga ministan Najeriya dake lura da masu zama a kasashen waje da kuma sauran kungiyoyi makamantansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.