fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yan Najeriya miliyan 25 za su rika biyan N4,000 duk wata don amfana da sabon tsarin wutar lantarki mai amfani da hasken rana

Kimanin yan Nijeriya miliyan 25 da aka shirya za su ci gajiyar tsarin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a duk faɗin ƙauyukan karkarar ƙasar wanda ake sa ran za su ringa biyan N4,000 kowane wata.

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta fara girka aikin hasken rana na Naira biliyan 140 ga iyalai miliyan 5 a yankunan marasa galihu da na karkara daga makon farko na Disamba.
Gwamnatin tarayya ta lura cewa wannan shirin ci gaba ne na aiwatar da tsarin tattalin arzikin dorewa (ESP) na gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Hukumar wutar lantarki ta karkara (REA) ce ta aiwatar da wannan shirin.
A wata sanarwa a ranar Lahadi, Laolu Akande, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya ce wadanda za su ci gajiyar shirin mai amfani da hasken rana, mai take Solar Power Naija, ana sa ran za su rika biyan N4,000 duk wata har tsawon shekaru uku.
Har ila yau, ana sa ran aikin kafa hasken rana ya samar da ayyuka kusan 250,000 ciki har da na masana’antu, harhadawa, girke-girke, kulawa da tsarin biyan kudi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Kungiyar magoya bayan Tinubu ta bayar da shawarar ya dauki Gwamna Elrufai a matsayin mataimakinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.