fbpx
Thursday, August 18
Shadow

‘Yan Najeriya Miliyan 79 ke cikin matsanancin Talauci>>Bankin Duniya

Wani sabon rahotan Bankin Duniya ya ce Najeriya ce ƙasa mafi yawan matalauta a ƙasashen kudu da hamadar sahara, wanda ƴan ƙasar miliyan 79 a 2018 ke cikin matsanancin talauci.

Najeriya ke da kashi 20 cikin 100 na matalauta a yankin, kamar yadda rahotan bankin kan talauci ya nuna.

Sannan rahoton ya kara da cewa annobar korona za ta sake tursasa wa mutum miliyan 40 shiga matsanancin ƙangin talauci a kudu da hamadar sahara.

Ya ce, “Kusan rabin mutanen da ke cikin talauci a kudu da hamadar saharar Afirka na rayuwa ne a ƙasashe biyar da suka hada da Najeriya da DR Congo da Tanzania da Ethiopia sai kuma Madagascar.

Karanta wannan  An shawarci Peter Obi ya nemi naira biliyan hamsin idan har yanaso ya kayar da Tinubu a zaben 2023

“A Najeriya, yankunan arewaci talaucin ya fi kamari, yayinda a yankunan kudu da garuruwan bakin ruwa abin da dan sauki.”

Bankin duniya ya ƙiyasta cewa annobar Covid-19 za ta sake jefa karin mutum miliyan 88 zuwa 115 cikin matsanancin talauci a wannan shekarar, adadin da ya ƙiyasta zai karu zuwa miliyan 150 a 2021, ko da yake ya danganta na yanayin tattalin arzikin ƙasashe

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.