Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta ce ‘yan kasar na kashe tsakanin dala biliyan daya da miliyan dari biyu zuwa dala biliyan daya da miliyan dari shida a duk shekara wajen neman lafiya a wata kasashen waje.
Ministan yada labarai da al’adu na kasar, Alhaji Lai Mohammed, ne ya sanar da hakan lokacin da ya kai ziyarar aiki zuwa wani asibitin Duchess da ke Lagos.
Ya ce, gwamnatin tarayyar na kokari wajen ganin ta dakatar da irin tafiya wadda ya bayyanata a matsayin abin da ke tatse asusun ajiyar kudaden waje na kasar.
Lai Mohammed, ya ce akwai tanade tanade masu kyau da dama da fannin asibitoci masu zaman kansu ke da su kamar irin asibitin Dutchess don hana irin wannan tafiya.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu gwamnatin tarayya ta zuba jarin dala miliyan 22 ta hanyar hukumar zuba jari ta Najeriya a cibiyoyin bincike biyu daya a Kano da kuma Umuahia da kuma cibiyar kula da masu cutar daji a Legas.