fbpx
Friday, June 9
Shadow

‘Yan Najeriya na yi wa gwamnatin Buhari shaguɓe kan kama Akanta Janar da EFCC ta yi

An wayi garin Talata 17 ga watan Mayun 2022 ƴan Najeriya suna ta mayar da martani kan kamun da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon ƙasa wato EFCC ta yi wa Babban Akantan kasar, bisa zarginsa da almundahanar kuɗi har naira biliyan 80. 

Hukumar, a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta kama Ahmed Idris ne a ranar Litinin a Kano da ke arewacin kasar.

EFCC na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.

Ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.

An kama Ahmed Idris bayan ya ƙi amsa gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Dandalin sada zumunta na Tuwita da Facebook sun zama manyan wuraren da ƴan ƙasar suka bazama suna bayyana ra’ayoyinsu a kan wannan lamari da ya kunno kai.

Maudu’ai biyar ne da suka danganci batun suke tashe a Tuwita da suka hada da #80bn da #Ahmed Idris da #EFCC da #Accountant General da kuma #ASUU, inda dubban mutane ke tattaunawa.

A dandalin Facebook kuwa kusan mutum 25,000 ne ke tsokaci kan batun da safiyar Talatar.

Mutane sun fi mayar da hankali ne wajen yi wa Shugaba Buhari shaguɓe tare da alaƙanta batun da yajin aikin da malaman jami’a ke yi a halin yanzu, wanda ya sanya ɗalibai zaman gidan tilas.

Yayin da wasu kuma suke ganin abin kunya ne a ce ana samun irin wannan lamari na almundahana a gwamnatin Buhari, wacce tun kafin kafuwarta ta dinga da’awar cewa za ta yi yaƙi da cin hanci da rashawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *