Sunday, May 31
Shadow

‘Yan Najeriya sun aike da sakonni sama da biliyan 1 a wata guda tunbayan gabatar da tsarin tura sako kyauta >>> MTN

Kamfanin MTN Nigeria ya tattara sakonnin da aka tura ta hanyar tsarin da ya bada dama na aike sakonni kyauta har sama da biliyan 1 a Najeriya.

Rahoton da Q1 na MTN ya nuna cewa sama da biliyan daya ne masu aika sakonnin suka aika a cikin makonni hudun farko na fara gabatar da sakonnin SMS kyauta wanda kamfanin ke bada damar aika sako 10 a kowacce rana har zuwa adadin 300  a kowane wata.

Tsarin wanda kamfanin MTN ya gabatar ya bayyana cewa sama da mutum miliyan 70 da sukai rijista nada damar aike sakon karta kwana kyauta har 300 a wata.

Wannan wani ɓangare ne na ‘Y’ello Hope Package’ wanda aka tsara don baiwa ‘yan kasa damar aike sako a sakamakon bullar cutar coronavirus, wanda hakan zai taimaka wajan Isar da sakonni don dakile yaduwar cutar Covid-19.

Idan zaku iya tunawa a makwannin baya Minisatan harkokin sadarwa ya bi sahun masu kiran kamfanin da su baiwa ‘yan Najeriya wata dama da zasu rage radadi na zaman kulle da suke ciki, daga bisani ne kamfanin ya gabatar da tsarin aika sako kyauta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *