fbpx
Monday, March 1
Shadow

Yan Najeriya sun gamsu da gwamnatin APC kuma alamu masu karfi na nuna zamu yi nasara a 2023>>Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai alama me karfi dake nuna Jam’iyyar su ta APC ce zata yi nasara a zaben shekarar 2023.

 

Ya bayhana cewa hakan ya biyo bayan Miliyoyin ‘yan Najeriya ne dake tururuwar sabunta rijista da jam’iyyar a yanzu haka yake gudana. Gwamna Ganduje yace ‘yan Najeriya sun saka ido inda suka lura da yanda gwamnatin APC ke ayyukanta kuma sun gamsu da ita.

 

Hutudole ya ruwaito muku cewa gwamnan yace ‘yan Najeriya sun aminta da cewa APC ce zata kai Najeriya tudun Mun tsira. Ya bayyana hakane bayan da ya sabunta rijistar sa ta APC a mazabar Ganduje cikin gari dake karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar ta Kano.

 

Gwamnan ya kuma yi kira ga jama’a su fito su sabunta rijistar tasu ta jam’iyyar.

“The last time the exercise took place was in 2014 and since then, we have a few people that left the party, and we have so many more that have joined the party.

 

“The exercise is important as the party is growing due to performance across the country,” he said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *