Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya ce za a debo ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje sannan za a killace su na tsawon mako biyu a Abuja, babban birnin kasar.
Sai dai ‘yan Nijeriya sun ce bayan saukarsu a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da misalin karfe 1:30 na ranar Juma’a babu wanda ya tarɓe su.
Sun yi korafin cewa kusan 90% daga cikinsu mazauna Jihar Legas ne kuma zasu fuskanaci matsala yayin komawarsu Legas din idan wa’adin killacewarsu ya kare saboda haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi.
Komawarsu kasar na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan wani jirgin ya sauke wasu 256 daga Daular Larabawa.