fbpx
Thursday, May 26
Shadow

‘Yan sa-kai sun ƙwato mutum 17 daga hannun ‘yan fashin daji a Jihar Neja

‘Yan banga ko ‘yan sa-kai a Jihar Neja sun afka sansanin ‘yan fashin daji tare da ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su a Dajin Zago, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Wani da aka gudanar da aikin da shi da kuma ya nemi jaridar ta ɓoye sunansa ya tabbatar da ceto mutanen a fadar basaraken Etsu Yaba da ke Abaji, Alhaji Abdullahi Adamu, inda aka kai mutanen ranar Alhamis.

Yankin Zago na maƙwabtaka da Ƙaramar Hukumar Abaji da Birnin Tarayya Abuja.

“Mun shirya mu da kanmu kuma muka shiga dajin, amma da suka gan mu sai suka fara harbe-harbe. Mu kuma har sai da muka kai wajensu. Sai kuma suka fara guduwa,” in ji shi.

Karanta wannan  Labaran ƙaryar da aka yaɗa kan cire gwamnan CBN ya yi tashe a Tuwita

Ya ƙara da cewa: “Mun ga mutum 17 a ɗaure, muka kwance su, muka ɗebo bindigogi kuma muka kawo wa mai martaba Etsu Yaba.”

Sarkin ya yaba wa dakarun, yana mai cewa “korar ‘yan fashin za ta daɗaɗa wa mazauna masarautarsa tare da ci gaba da ayyukansu na noma cikin kwanciyar hankali”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.