Yan sanda biyu sun rasa rayukansu a wani hadari da ya hada da ayarin motocin Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a ranar Talata.
Oshiomhole da tawagar yakin neman zaben APC na kan hanyarsu ta zuwa Usen a karamar hukumar Ovia kudu maso gabas ta jihar Edo lokacin da hatsarin ya faru.

Da yake magana a kan lamarin, dan takarar gwamna na APC, Osagie Ize-Iyamu, ya ce za a iya fassara hatsarin a matsayin yunkurin kashe Oshiomhole.
Ya kuma sanar da dakatarwa na awanni 24 na kamfen dinsa don girmama jami’an da suka mutu.