fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Yan sanda a Legas sun lalata miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai N10m

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas tare da hadin gwiwar ‘yan uwanta jami’an tsaro a ranar Talata sun lalata wasu miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 10.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka, DCP Ahmed Kotangora ne ya jagoranci tawagar zuwa rumbun da ke Ewu-Elepe da ke wajen Ikorodu a jihar Legas, domin lalata magungunan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, ‘yan sanda, jami’an NDLEA, NAFDAC, Neighborhood Watch da kuma jami’an yaki da cin hanci da rashawa ne suka sa ido kan atisayen.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Yawancin masu laifin dake gidan yarin da aka ajiye Abba Kyar na Kuje sun tsere bayan 'yan bindiga sun kai masu hari

DCP Kotangora, wanda ya wakilci kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas, CP Abiodun Alabi, ya ce atisayen ya bi umarnin kotu na lalata miyagun kwayoyi da tawagar ‘yan sanda ta Rapid Response Squad suka kwato a jihar a watan Afrilu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.