fbpx
Monday, August 8
Shadow

Yan sanda biyu sun mutu yayin Da ‘Yan Bindiga suka Kai hari Ofishinsu a jihar Edo

Jami’an ‘yan sanda biyu, Sufeto, da wani dan sanda sun mutu lokacin da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai hari ofishin’ yan sanda da ke Igueben, hedkwatar gudanarwa na karamar hukumar Igueben ta jihar Edo.
An tattaro cewa jami’ai da dama sun samu raunuka daban-daban yayin da ‘yan daban suka tafi da makamai da alburusai.
An kuma tattaro cewa maharan sun afkawa ofishin ‘yan sanda da misalin karfe 8 na dare, inda suka yi amfani da nakiya kafin su samu damar shiga.
An ce an ijiye jami’an da suka mutu a dakin ijiye gawawwaki.
A halin da ake ciki, matasan yankin sun fito kan tituna don nuna rashin amincewarsu da harin wanda suka ce ba ‘yan asalin yankin ne suka kai shi ba.
Matasan sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta binciki wannan harin, suna zargin cewa aikin mamaya ne daga waje.
Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ta jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor, ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Johnson Kokumo, zai magance lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Shugaba Buhari yace a lahire ne kadai babu matsar tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published.