Sufeto janar na ‘yan sanda (IGP), Mista Mohammed Adamu, a ranar Talata ya ce an kama mutane 12 da ake zargi da hannu a hare-hare da kone wasu ofishoshin ‘yan sanda a jihar Benin.
jami’in hulda da jama’a na rundunar (FPRO), Mista Frank Mba shine ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce, an kuma gano wasu bindigogin AK47 guda biyar, wadanda aka sata daga ofisoshin ‘yan sandan da aka lalata.
Haka zalika Safeto janar na ‘yan sanda ya aike da Jami’ai domin tabbatar da tsare lafiya da dukiyoyin al’umma a fadin kasar.