fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

‘Yan sanda sun Cafke mutum 4 bisa laifin yunkurin sai da wata Mota mallakar Kamfanin Dangote

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Neja ta ce ta kama wasu mutane hudu a karamar hukumar Gurara a jihar, da ake zargi suna da hannu a wata badakalar sayar da trailer din Kamfanin Dangote.

‘Yan sanda sun kuma ce mutanen hudu da suka hada da wani ma’aikacin kamfanin suna da hannu wajen karkatar da buhunan siminti guda 900 ba bisa ka’ida ba.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar, PPRO, ASP Wasiu Abiodun ya fitar ya ce, kamon ya biyo bayan wani rahoto da aka sanar da hukumar ‘yan sandan jihar.

PPRO  ya bayayana cewa ‘yan sanda sun damke Saidu Ayaba da wata motar tirelar mallakar kamfanin Dangote wacce ba komai a cikin ta, motar mai lamba  KMC 544 XA a Dikko junction, dake karamar hukumar Gurara, a lokacin da ake ƙoƙarin sayar da motar.

Abiodun ya bayyana cewa a yayin yin tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin cewa a ranar 26 ga Mayu, 2020, an ba shi amanar buhunan siminti guda 900 don kaisu jihar Kano.

Inda ya kara da cewa, maimakon yin abin da kamfaninsa ya sanya shi yayi wajan Isar da kayan inda ya dace, amma hakan sai ya faskara inda suka hada baki da sauran ukun da ake zargi, inda suka  sayar da buhhunan simintin ga wani Alhaji  Aminu dake karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara akan kudi Naira N2,160,000.00k

Karanta wannan  Bidiyo: Bayan shekara daya, An kama wanda ya kashe Ahmad Gulak

Sauran mutane ukun da ake zargi su ne Habibu Isah na Shiyar Numo, karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara sai Mudashiru Dahiru dake karamar hukumar Madobi a jihar Kano, da kuma Abdullahi Mohammed dake Buratai, a karamar hukumar Biu a jihar Borno.

Haka zalika raoton ya bayyana cewa “Habibu Isah da Mudashiru Dahiru sun taimaka wajen karkatar da siyar da siminti ga wani mai suna Aminu ‘m’ na Tsafe dake jihar Zamfara, Bayan sun sayar da buhhunan Cimintin sun kuma kara yin wani yunƙuri na siyar da motar ka cokan.

Hukumar ‘yan sandan ta bayyana cewa Abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da motar tirela da buhu bud 754 na ciminti.

Ya ce yanzu haka ana kan binciken lamarin kuma za a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu da zarar an kammala bincike.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.