fbpx
Friday, February 26
Shadow

‘Yan Sanda sun cafke wani dake ikirarin Shi malamine, Yusuf da kan mutum

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Osun sun cafke wani malami, Tiamiyu Yusuf, dauke da kan mutum a yankin Iwo.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, CP Wale Olokode ya tabbatar da cafke wanda ake zargin.
An dauke wanda ake zargin daga hedikwatar ‘yan sanda na Shiyya ta Iwo zuwa sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar da ke Osogbo, don ci gaba da bincike.
A tattaunawar da akayi da Tiamiyu a Hedkwatar ‘yan sanda, ya furta cewa ya sayi kan mutum kan kudi N20,000 daga abokinsa.
“Gaskiya ne. An kama ni da kan mutum. Na saya wa wani ne. Yana son amfani da shi don tsafin kudi. Na saya masa a kan N20,000 ”.
CP Olokode ya ce an kuma kama sauran wadanda ake zargi da alaka da lamarin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *