Rundunar ‘yan sanda reshen babban birnin tarayya Abuja, ta yi nasarar cafke wani da ake zargi, Hamisu Tukur, mai shekaru 25, bisa zargin satar motar hukumar kiyaye haddura ta kasa, (FRSC) a Hedikwatar ta da ke Abuja.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda dake babban birinin tarayya Abuja DSP Anjuguri Manzah ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar.
A cewarsa, jami’an ‘yan sanda daga ofishin hukumar dake Bwari sune suka cafke wanda ake zargin a ranar Asabar a lokacin da suke kan gudanar da aikin tsaro, bayan da su ka samu kiran waya daga hedkwatar Hukumar kiyaye hadura kan lamarin.
Ya kara da cewa abubuwan da aka samu a hannun wanda ake zargin sun hada da farar Toyota Hilux- mai lamba HQ-26RS da kuma mukulli guda daya.
A karshe ya tabbatar da cewa dazarar hukumar ta gama bincike zata gurfanar da wanda a ke zargi a gaban kotu, kamar yadda jaridar Tribune ta labarta mana.